Akwai yuwuwar ASU zata tafi yajin aiki

0 2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Mambobin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi gargadin cewa za ta tafi yajin aiki idan har gwamnatin tarayyya ba ta yi gaggawar magance matsalolin da jami’o’in ke fuskanta ba. Wannan batu ya biyo bayan gazawar da gwamnatin mai ci ta yi na aiwatar da yarjejeniyar da aka shiga da kungiyar a shekarar 2013. Shugaban kungiyar Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayyana cewa, da yawa daga cikin bangarorin yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin a shekarar 2009 har yanzu ba su samu kulawa ba. Ya kara da cewa, a cikin Naira biliyan 30 din da gwamnati ta ware domin a biya bukatun kungiyar, naira miliyan 13 kawai aka saki aka yi amfani da shi. Ya bayyana cewa wannan gwamnati ta saba yarjejeniyar da ta yi kunnen uwar shegu da bukatunsu kuma sam baza su iya yarda da hakan ba.Kungiyar ta ASUU dai ta yi yajin aiki a shekarun 2012 da 2013 duk a kan wannan yarjejeniya inda ta samu nasarar tilastawa gwamnatin baya biya mata wasu daga cikin bukatunta da ta yarda da su a yarjejeniyar

Get real time updates directly on you device, subscribe now.