Akwai Yiwuwar a Samu Raguwar Farashin Man Fetur – ‘Yan Kasuwar Mai

0 2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Babban sakataren kungiyar ‘yan kasuwa masu
hada hadar man fetur Alhaji Danladi Fasali ya
musalta batun karin farashin mai da ke ta zagaye
a kafafen yada labarai a yanar gizo inda ya ce ga
dukkan alamu ma sai dai su rage farashin duba
da yadda suke ta kawo kaya.
Ya yi wannan batu ne a yayin da yake amsa
tambayoyin wakilin kafar yada labarai ta Muryar
Amurka akan jita jitan karin farashin mai.
Fasali ya ce farashin da suke sayar da mai a
yanzu haka ya kai makura.
Ya kara da cewa su na da shirin sayar da man
kasa da farashin gwamnati idan kayan su na
gaba suka iso nan da sati mai zuwa. Ya ce ko
yanzu ma akwai wasu ‘yan kasuwa da ke sayar
da man kasa da farashen gwamnati a jahar
Legas inda ya bayarda misalin kamfanin
“intergrated” dake sayar da man akan naira dari
da talatin da daya maimakon dari da arba’in da
biyar.
Yace farashin man kara sauka ya keyi ba wai
yana karuwa ba ne. Ya ce tun da aka baiwa
kamfanoni damar su shigo da man fetur din
yadda suka ga dama, toh kamfanoni da yawa
zasu fara sayar da man fetur din kasa da farashin
NNPC.
Ga me da wahalar da ake fuskanta na samun
dala, fasali yace akwai shirin da babban bankin
kasa CBN ta ke da shi na tallafawa masu shigo
da man Fetur din, inda ya ce da yawa daga
cikinsu ma sun yi nasu yarjejeniyar ne da
kamfanoni kasashen wajen ta yadda ba sa
bukatar dala daga babban bankin sai dai su
shigo da na su.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Get real time updates directly on you device, subscribe now.