Akwai bukatar buhari ya yi awon gabada wasu jaminan sa

0

Tun bayan komawar Shugaban
Najeriya Muhammadu Buhari gida,
bayan shafe watanni yana jinya a
birnin Landan, daya daga cikin abin
da aka zuba ido akai shi ne yi wa
gwamnatinsa garanbawul, domin fitar da wasu da ake yi wa kallon sun
zame wa gwamnatin karfen-kafa.

Malam Auwal Musa Rafsanjani,
shugaban kungiyar CISLAC, mai sa
ido kan ayyukan majalisar dokoki a
Najeriya, ya shaida wa BBC cewa
lallai akwai bukatar Shugaba Buhari
yayi awon-gaba da wasu da ke ja wa
gwamnatinsa bakin jini.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Source: bbc