Adaddin yan Nigeria yakai 193 da dubu 392 da 517

0

Sabbin alkauma da hukumar kididdiga ta kasa ta fitar na nuna cewa adadin ‘yan Nijeriya ya kai miliyan 193 da dubu 392 da 517 (193,392517).

Wannan dai na nuna cewa an samu karuwar jama’a da fiye da miliyan hamsin a cikin shekaru 10, wato tun bayan kididdigar da aka yi a shekarar 2006 wanda ya nuna cewa adadin ‘yan Nijeriya miliyan 140 ne da ‘yan kai.

A wadannan sabbin alkaluma, jahar Kano ita ce ta daya da yawan mutane 13,076,892, inda jahar Lagos ta ke a sahu na biyu da yawan mutane 9,113,605.

Sai dai wannan adadi da jahar Lagos ya sha bambam da wanda gwamnatin jahar da kuma majalisar dinkin duniya ta fitar wanda ya kiyasce cewa mutanen jahar ta Lagos sun kai miliyan 22.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

A alkaluman kididdigar 2006, an samu adadin mutanen Kano guda 9,401,288, yayin da na jahar Lagos ya ke 12,550,598.
Alkaluman sun nuna cewa akwai
mazaje 98,630,184 da mata guda 94,762,333 a fadin Nijeriya.

Yara kanana su ne mafi yawa a cikin ‘yan Nijeriya, inda aka kiyasce cewa akwai kimanin yara ‘yan shekaru tsakanin 0 da 4 guda 31,116,156, sannan yara tsakanin shekaru 5 da 9 guda 27,549,964.

Alkaluman sun nuna cewa duk da matsalar Boko haram da ta addabi yankin arewa maso gabashin kasar nan, an samu karuwar adadin mutane a yankin.

Jahar Kaduna ita ce ta uku da
mutane 8,252,366, inda jahar Oyo ke bin ta da mutane 7,840,864. Jahar Katsina ita ke gida na 5 da adadin mutane 7,831,319.