Trump ya Rasa Rinjaye A majalisa

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zaben tsakiyar zangon ‘yan majalisa wata babban nasara ce ga jam’iyyarsa, duk da cewa ya rasa rinjaye a majalisar wakilai.

Jam’iyyarsa ta Republican ta yi nasara rike rinjayenta a majalisar dattawan kasar, saboda zazzafar yakin neman zabe, ayayin da ita kuma Democrats ta yi babban kamu a majalisar wakilai.

Kafar talabijin na CBS ya yi hasashe cewa jam’iyyar Democrats za ta samu rinjaye, inda za ta kwace jagorancin majalisar daga hannu Republican bayan shekara 8.

Baban jami’i a jam’iyyar Democrats Tom Perez ya ce fatan da suke shi ne samun kuri’u da yawa, kuma Amurkawa sun zabi jam’iyyar a fadin kasar.

Bayanai na nuna cewa mutane sun fito sosai, a zaben da ke kasance mai muhimmaci, da kuma zai daidaita manufofin gwamnatin Mista Trump a cikin shekaru biyu nan gaba.

Zaben ya kuma hada da na gwamnoni a jihohin kasar 36.

Masu kada kuri’a a jihohin kasar sun yanke hukunci ne a kan abubuwa daban-daban

A florida kuma, masu zabe sun amince da shirin dawo da ‘yancin kada kuri’a ga fursunoni.

Wannan layi ne

Kalubale

Sakamakon wannan zabe ya nuna cewa Democrats na da dama kalubalantar manufofin Mista Trump, don haka babbar koma baya ce ga gwamnatinsa.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Babban abin da ‘yan Republican suka sanya a gaba yanzu shi ne karfafa karfin fada a ji a zauran majalisar dattawa.

Ba za dai a kara zaben shugaban kasa ba sai a shekakar 2020, amma kuma ana kallon zaben na jiya Talata a matsayin raba gardama ga shugaban kasar mai janyo ce-ce-ku-ce.

A lokacin Yakin neman zaben, Trump ya gabatar da batutuwan shige da fice da tattalin arziki domin jamiyyar Republicans ta samu goyon bayan jama’a, yayinda jamiyyar adawa ta Democrats ta maida hankali kan tsarin kiwon lafiya da kuma dacewar Donald Trump da zama a kujerar mulki.

Wannan layi ne

Mata sun taka rawar gani

‘Yan takara mata su bada mamaki a wannan lokaci, inda suka taka rawar gani wajen samun nasarori a kujerun wakilai abin da ya sa ake ganin wannan shekarar ta su ce.

Daga cikin matan da suka yi takara akwai Alexandria Ocasio-Cortez, mai shekara 29 da ta samu nasarar lashe kujerar majalisar wakilai a karkashin Democrats, sannan ta kasance mace ta farko mafi kanranci shekaru da ke samun wannan nasarar.

Sharice Davids daga Kansas da kuma Debra Haaland ta New Mexico sun zama ‘yan asalin Amurka na farko da suka lashe kujerun majalisar wakilai a inuwar Democrats.

Hakazalika akwai mata musulmi Ilhan Omar da Rashida Tlaib da suka kafa tarihi nasara a jihohin Minnesota da Michigan.

Ita ma Ayanna Pressley ta lashe kujerar Massachusetts’ a matsayin mace bakar fata ta farko.

Shugaban jam’iyyar Democrats a majalisar wakilai Nancy Pelosi ta gode wa Amurka da basu goyon baya.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.