Muna Masu Baku Hakuri

0 42

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Assalamu Alaikum barkanmu da kasancewa a wannan lokacin da fatan kuna lafiya.

Dalilin rubuta wayannan post din shine:-

Wasu mawaka sun nuna rashin jin dadinsu akan dora musu wakokinsu a shafukan yanar
gizo kuma suka umarcemu da mu daina dorawa kuma mugoge wayanda muka dora.

Amma tun farko laifinmu ne da bamu tambayesu ba kuma ba tare da umarninsu ba, kuma muna nema afuwarsu a bisa haka.

Sunnuna suna bukatar duk mai san wakokinsa da yaje shafinsu na iTunes.com Ko Amazon.com domin ku nemi wakokinsu a can
Duk waka daya 200 Album kuma 1500 ko Channel Dinsu Na YouTube.

Daga Yanzu muna bada hakuri da kada wanda ya kara zuwa ya tambayemu wakokinsu ko
yaushe album dinsu zai fito sai sai kubisu ta social dinsu na instagram ko facebook Allah ya
bada sa,a.

Wayannan Mawakanko Sune:-

1- Nura M Inuwa
2- Umar M Shareef
3- Adam A Zango

Amma kuma sauran mawakan bamuji ta bakinsu ko muce ra’ayinsu suma, shin mucigaba da dorawa ko mudaina muna nan muna tutubarsu kuma yanzu haka suma wakokinsu mun gogesu a wannan shafin namu.

Mawakan Sune Kamar Haka;-

1- Husaini Danko
2- Ado Gwanja
3- Abdul D One
4- Ahmad M Sadiq
5- Sayyid Gadan Kaya
6- Faruq M Inuwa

Yanzu Mawakan Da Suka Bada Dama Mu Dora Wakokinsu Sune:-

1- Saniyon M Inuwa
2- Isah Ayagi
3- Shamsu Alale
4- Hamisu Breaker
5- Sammani AA
Da Sauransu.

Ba wai munyi wannan post din bane dan wani abu ba munyisa ne dan kada masoya kuzo kuna tambayarmu sababbin kayansu, ko kuma bata musu suna, Kullin burinmu ganin cigaban mawakanmu na hausa shiyasa kawai amma badan hakaba
akwai abubuwa da dayawa zamuyi.

Kuma a shirye muke da kowane mawaki idan yana bukatar muna doramasa wakokinsa a wannan shafin namu kawai na data zai biya ba tsada wata rana sai labari.

Idan kuka duba sauran mawakan Kudu Da na Hausa Hip Hop Idan Kukaji Abinda suke biya domin ai musu promo din wakokinsu.

Akwai shafukan da dayawa free suke dorawa Amma wajan banbancin shine shafin da yafi
shahara nane zakuga ana biya domin mutum yanso yaga wakarsa a babban shafi.

Allah Yasa Mudace Ameen

Daga Arewaclass C.E.O

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram